Kara Surah Al-Infitar

Surah Al-Infitar (الإنفطار) ita ce surah na Makka ta Alkur'ani tana da ayoyi 19. Ku karanta, ku saurari kuma ku hadda wannan surah tare da kayanmu masu hulɗa.

An sabunta a 28 Oktoba 2026 00h24

📖 Karatu minti 1

Surah Al-Infitar cikin lambobi

Tsarin saukarwa
Saukarwa n° 82 / 114
(na Makka)
81
kalmomi
-88.7% vs matsakaici
343
haruffa
-88.8% vs matsakaici
1
min karantawa
19
ayoyi
-65.3% vs matsakaici

Yawan amfani da kalmomin bincike

الله 1
رب 1

Haruffa da yawa suke fitowa

ل
31
#1
ا
28
#2
م
27
#3
ن
23
#4
و
22
#5
الإنفطار · Juz 30
Kewaya
Alamomi
Sauti
Hadda
Nuni
◄ Kara Surah Al-Infitar ►
سورة الإنفطار
Juz 30 27.8% (157/564)
Hizb 59 56.9% (157/276)

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنفَطَرَتْ ﴿1﴾

Idan sama ta tsãge.

وَإِذَا ٱلْكَوَاكِبُ ٱنتَثَرَتْ ﴿2﴾

Kuma idan taurãri suka wãtse.

وَإِذَا ٱلْبِحَارُ فُجِّرَتْ ﴿3﴾

Kuma idan tẽkuna aka facce su.

وَإِذَا ٱلْقُبُورُ بُعْثِرَتْ ﴿4﴾

Kuma idan kaburbura aka tõne su.

عَلِمَتْ نَفْسٌۭ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ ﴿5﴾

Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلْإِنسَـٰنُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ ٱلْكَرِيمِ ﴿6﴾

Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.

ٱلَّذِى خَلَقَكَ فَسَوَّىٰكَ فَعَدَلَكَ ﴿7﴾

Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.

فِىٓ أَىِّ صُورَةٍۢ مَّا شَآءَ رَكَّبَكَ ﴿8﴾

A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.

كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِٱلدِّينِ ﴿9﴾

A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!

وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَـٰفِظِينَ ﴿10﴾

Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.

كِرَامًۭا كَـٰتِبِينَ ﴿11﴾

Mãsu daraja, marubũta.

يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ ﴿12﴾

Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.

إِنَّ ٱلْأَبْرَارَ لَفِى نَعِيمٍۢ ﴿13﴾

Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.

وَإِنَّ ٱلْفُجَّارَ لَفِى جَحِيمٍۢ ﴿14﴾

Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.

يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ ٱلدِّينِ ﴿15﴾

Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.

وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَآئِبِينَ ﴿16﴾

Bã zã su faku daga gare ta ba.

وَمَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ ﴿17﴾

Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?

ثُمَّ مَآ أَدْرَىٰكَ مَا يَوْمُ ٱلدِّينِ ﴿18﴾

Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?

يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌۭ لِّنَفْسٍۢ شَيْـًۭٔا ۖ وَٱلْأَمْرُ يَوْمَئِذٍۢ لِّلَّهِ ﴿19﴾

Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.

بسم الله الرحمن الرحيم Lit 21 Jumada al-Awwal
الاثنين 21 جمادى الأولى
التربيع الأخير Kwata na Ƙarshe Rana 22.5 / 29.5
Haske 46%
Wata Sabo a cikin kwana 7
الحمد لله Alhamdulillah - Godiya ta tabbata ga Allah

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِىِّ ۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ صَلُّوا۟ عَلَيْهِ وَسَلِّمُوا۟ تَسْلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikunSa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Al-Ahzab 33:56

Salati ga Manzon Allah